Mutane 28 suka halaka kana wasu 64 suka kamu da ciwo sanadiyar barkewar cutar gubar dalma a jihar.
Lamarin ya faru ne a wani wurin da ake hako ma'adanan kasa a kauyen Achara cikin yankin karamar hukumar Rafi. Wadanda suka mutu da wadanda suka kamu da ciwo dukansu yara ne 'yan kasa da shekaru biyar. Hakazalika hukumomin kiwon lafiya sun tabbatar cewa sama da dabbobi 100 ne suka mutu a sakamakon bullar cutar.
Dr Usman Muhammad daraktan matakin farko na ma'aikatar kiwon lafiyar jihar yace cutar ta fara yaduwa ne tun a 'yan watannin da suka gabata amma sai yanzu jami'an kiwon lafiya suka farga. Bayan su daga ma'aikatar kiwon lafiya sun isa wurin sun tabbatar da abun dake faruwa sun sanarda ma'aikatar kiwon lafiya ta tarayya.
Dr Muhammad yace sun shiga wayar da kawunan mutane saboda kauyawan sun dauka wai mayu ne suke kashe masu yara. Yanzu dai kowa ya san abun dake faruwa kuma an dakatar da hakan ma'adanai a kauyen tare da sauyawa mutanen kauyen matsuguni..
Shugaban karamar hukumar Rafi Sahabudeen Isa yace sun dauki wasu matakai a hukumance. Mataki na daya shi ne rufe inda ake nikan ma'adanan. Sun hana anfani da rafin da ake wanke ma'adanan kana mutanen kauyen an mayar dasu wurin da bashi da nisa da gonakansu.
Daga bisani wadanda suka kamu da cutar an turasu zuwa wani asibiti a jihar Zamfara domin samun kulawa ta musamman.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.