Gwamnatin Jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya, ta sanar da sassauta dokar hana fita inda aka mayar da ita daga karfe 2 na rana zuwa 6 na yamma.
A ranar 5 ga watan Agusta gwamantin ta saka dokar hana zirga-zirga bayan da zanga zangar da ake yi ta jirkice ta koma tarzoma a yankin Jos ta Arewa da kewaye.
“Bayan samun daidaituwar al’amura a yankin Jos-Bukuru, gwamnatin jihar Filato ta sassauta dokar hanafita ta sa’o’i 24 da aka saka.” Sanarwar da Darektan yada labarai Gyang Bere ya fitar ta ce.
A cewar Bere, Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ya ba da wannan umarni ne bayan da ya tuntubi jami’an tsaro.
Gwamnan ya kuma kara jaddada muhimmancin zaman lafiya yana mai tabbatar wa da al’umar jihar cewa gwamnati a shirye take ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a.