An Samu 'Yan Gudun Boko Haram Fiye da 17,000 a Birnin Yola

Yara da manya masu gudun Boko Haram.

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta tabbatar da cewa a cikin su akwai yara fiye da 6,000.

Wata kididdigar hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta nuna cewa yanzu haka akwai mutane sama da dubu goma sha bakwai masu zaman gudun 'yan Boko Haram a birnin Yola, fadar jahar Adamawa.

Kididdigar ta nuna cewa akwai yara kanana fiye da dubu shida a sansanonin 'yan gudun Boko Haram da aka kakkafa a garin Yola.

Wadannan dubban mutane sun gudu sun bar gidajen su ne sakamakon kwace kananan hukumomin Madagali, da Michika, da Mubi ta Arewa, da kuma Mubi ta Kudu.

Babban jami'in hukumar NEMA mai kula da shiyyar arewa maso gabashin Najeriya Alhaji Muhammad Kanar ya bayyanawa wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz, irin kokarin da ma'aikatan su ke yi domin tallafawa mutane masu zaman gudun 'yan Boko Haram:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Gudun Boko Haram Sun Cika Birnin Yola Maki. - 2'39"