Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Sallar Neman Zaman Lafiyar Adamawa a Masallatan Jimeta da Yola


Musulmai wajen salla
Musulmai wajen salla

Tun da sayin safiyar jiya mutane suka yi cincirindo a masallatan Jimeta da Yola domin gabatar da sallar nafila da kuma yin addu'o'i na musamman akan halin da jihar ke ciki.

Sun roki Allah ya karesu ya kare kasar su kuma zasu bi umurni. Duk abun da aka fada masu zasu yi. Sun roki Allah ya gama du duk wadanda suke neman su cucesu.

Malam Ismail Modibo sakataren Musulman jihar Adamawa ya bayyana dalilin gudanar da addu'o'in. Yace sakamakon abubuwan dake faruwa a jihar da wasu wuraren yasa malaman jihar suka taru suka yadda su yi sallar idi tsakanin Jimeta da Yola jiya. Bayan haka a duk kananan hukumomi za'a yi sallar idin domin neman mafita zuwa ga Ubangiji.

Yace suna neman taimako daga Allah domin ya fitar dasu a cikin kangin da suka shiga.

Tuni dai wasu suka fara firgita a Yola lamarin da Abdullahi Damari na kungiyar kawo fahimta tsakanin kiristoci da musulmai yace bai dace ba. Gudu bashi da fa'ida domin sabili da gudun akan rasa rayuka da dukiya da muhallai. Yace a matsayinsu na musulmai duk inda suke Allah yana nan. Sabili da haka kowa ya tsaya inda yake ya cigaba da rokon Allah.

Yanzu dai akwai dimbin yara da aka rabasu da iyayensu. Wani yaro yace daga Askira yake. Bayan an kashe mahaifisa da wasu 'yanuwansa uwarsa da sauran 'yan uwan sun gudu. Shi ma ya tsallaka katanga ne ya samu ya tsere har ya iso Yola. Kawo yanzu bai san inda sauran 'yanuwansa suke ba.

An kiyasta cewa sama da mutum dubu ashirin suka fantsama cikin Yola yayin da wasu da dama suka nufi kasar Kamaru. Alhaji Muhammed Kanar jami'in hukumar dake bada agajin gaggawa a shiyar arewa maso gabas yace suna bi suna raba abinci da kayan kwanciya da kayan wanka.

Dangane da wadanda suke kasar Kamaru wata tawaga zata fara tafiya ta shirya yadda za'a dawo dasu gida.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG