A taron manema labaran da ya kira, reshen hukumar ta UN HCHR ko HCDH mai ofishi a birinin Yamai ya yi bayani akan mahimman abubuwan da suka wakana a Nijar a tsakanin watan Satumba zuwa Disamban 2022.
A bayaninsa, Wakilin hukumar UN HCRH, Omar Kebiwou Kalameu, ya ce “a wannan dan tsakani HCDH ta yi rajistar abubuwan tauye hakkin dan adam kimanin 351 da kuma ta’asa 349 daga cikinsu, kungiyoyin ta’addanci ne ke da alhakin aikata su wadanda suka hada da GSIM da EIGS, inda suka hallaka mutane a kalla 104 sannan suka sace wasu 167, yayin da suka raunata fararen hula 50 suka kuma aikata fyade sau 2 tare da yin kwace sau 28, suka kora dubun dubatar dabobi da kwace wa al’umma miliyon cfa. Kuma a daidai wannan lokaci tashin hankalin da ake fama da shi ya yi sanadin rufe makarantu 240 a gundumar Tera ta jihar Tilabery. Ko da yake mahukunta sun kafa cibiyoyin musamman domin karantar da yaran yankunan da ke fama da aika aikar ‘yan bindiga. Haka kuma an gano jami’an tsaro da take hakkin dan adam sau 2 a wannan yanki kamar yadda kuma bayanai ke nunin yadda hukumomi suka karfafa matakai domin tabbatar da tsaro.”
A ci gaban bayanan da ta tattara hukumar HCDH ta ce binciken da ta aiwatar abu ne da ke shafar wani bangare na yankunan wannan kasa sakamakon rashin wakilai a wurare da dama, amma kuma irin ababen da rahoton ya kunsa manuniya ce kan halin cin zarafin da jama’a ke fuskanta a fadin Nijar.
A hirar shi da Muryar Amurka, Shugaban kungiyar Voix des sans Voix, Alhaji Nassirou Saidou, ya ce talakawa da gwamnati ta Nijar ba za su karbi rahoton da hannun biyu ba ko a bashi muhimmanci da ya kamata, duk da tana hukuma ta MDD reshen Nijar.
Ya ce dole sai ta samu ta tattara bayanai a sauran jihohi da wannan abun ya shafa da ta ce ba ta da wakilai, wanda shi ya kawo rauni a cikin rahoton.
A shekarar 2019 ne aka cimma yarjejeniya a tsakanin MDD da gwamnatocin kasashe akan maganar fitar da rahoto a kowane wata 3 game da halin da ‘yancin dan adam ke ciki a kasashen da suka yi na’am da wannan sabuwar tafiya ta neman inganta yanayin ‘yancin dan adam.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5