An sami koma baya a shayar da yara nono

Wata mace tana ba yaro nono

Jami’an kiwon lafiya na jihar Naija sun ce an samu koma baya wajen shayar da jarirai da nonon uwa.
Jami’an kiwon lafiya na jihar Naija sun ce an samu koma baya wajen shayar da jarirai da nonon uwa. Wadanan jami’u sun ambata muhimancin shayar da nonon uwa ga jarirai musamman a cikin watanni shida na farko bayan haihuwa.

A cikin bayanin su, sun ce an samu koma baya da kashi 13 bisa dari na yawan uwaye masu ba jariran su nono yada ya kamata. Dr. Mohammed Ndagi, direktan sashen magunguna da sanadaren gina jiki na ma’aikatan lafiya a jihar Naija yace mata basu shayar da nono yadda ya kamata. Ya kuma ce kada a rika gauraya nonon uwa da ruwa ko da kowane abu idan za a ba dan jariri.

Your browser doesn’t support HTML5

Shayar da yara nonon uwa