Kwamishinan lafiya na jihar Borno Dakta Haruna Mshelia, ya tabbatarwa da Muryar Amurka cewa sun sami wata mata aka yiwa gwaji aka kuma tabbatar da kwayar cutar Lassa a tare da ita. Wadda yanzu haka aka kebe ta tare da bata kulawar da ta kamata.
Zazzabin Lassa, wanda wani nau’in bera ke yadawa, a baya ya haddasa mace-mace a sassan Najeriya. Na baya-bayan nan shi ne kashe mutane a kalla 16 da wani zazzabin da ake kyautata zaton na Lassa din ne ya yi a jihar Naija.
Tun a karshen shekarar da ta gabata ne cutar ta kunno kai inda mutane da dama suka kamu da ita yayin da wasu ma suka rasa rayukansu. Alamun kamuwa da cutar sun hada da zazzabi mai zafi da ciwon ciki da kuma kasala, idan yayi tsanani akan samu fitar jinni ta hanci ko kunne.
jami'an kiwon lafiya a Najeriya, sun ce tsabta na daga cikin matakin farko da mutane za su dauka domin kare kansu daga cutar.
Sannan akwai bukatar a daina barin abinci a bude musamman inda beraye ke shawagi.
Domin karin bayani ga tattaunawar Haruna Dauda da Dakta Mshelia, kwamishinan lafiya na jahar Borno.
Your browser doesn’t support HTML5