An gudanar da taron masu ruwa da tsaki da hukumar inganta zaman lafiya ta jihar tare da hukumar tsaro da hukumar ba da tallafi ga masu kananan masana'antu suka shirya a Jos domin tattauna hanyoyin inganta tsaro da rayuwar al'umma.
Sakataren gwamnatin jihar Rufus Bature ya ce gwamnati ta kirkiro tsare-tsaren samar da aikin yi wa al'ummarta. Ya kuma ce yau a jihar Filato an samu zaman lafiya da fatan zai zama na dindindin.
Shugaban hukumar samar da tsaro ta jihar Janar Stephen Gua'ar ya ce idan jama'a na da aikin yi ya yi imani tsaro zai tabbata ya na jaddada cewa idan mutum na da abin yi ba zai je neman fitina ba.
Shi ma shugaban hukumar inganta zaman lafiya Joseph Lemang ya ce makasudin taron shi ne su hada gwiwa da masu ruwa da tsaki wajen samun zaman lafiya mai dorewa.
Shi ko shugaban hukumar yaki da talauci a jihar Haruna Gutap ya ce akwai tsare-tsare da suka yi ta yadda al'umma da suka yi kungiyoyi za su samu gajiyar tallafin.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Facebook Forum