An Sami Wani Yaro Mai Shekaru Biyar Da Kwayar Cutar Ebola A Liberia

Liberia

Jami’an kiwon lafiya a Liberia, sun ce an samu wani yaro mai shekaru biyar da kwayar cutar Ebola, kwanaki kadan bayan mutuwar mahaifyarsa.

Wata mata mai shekaru 30 ta rasu a Monrovia a makon da ya gabata, wato ‘yan wasu watanni bayan da aka ayyana kasar ta Liberia a matsayin wacce ta shawo kan cutar.

Mutuwar matar ta biyo bayan rasuwar wasu mutane hudu a Guinea da ke makwabtaka da kasar ta Liberia.

Mataimakin Ministan kiwon lafiyar Liberia, Tolbert Nyenswah, wanda shi ke kula da fannin yaki da cutar ta Ebola a Liberia, ya ce an sake samu bullar cutar ce daga Guinea da ke makwabtaka da su.

Sai dai ya ce ba kamar a baya ba, yanzu Liberia na da shirin da zai iya dakile bullar cutar a kowane lokaci.

A watan da ya gabata ne Guinea da ke makwabtaka da Liberia ta kara samun sabbin masu kamuwa da cutar, lamarin da ya sa Liberian ta yi maza-maza ta rufe kan iyakarta da kasar, tare da tura kwararru a fannin kiwon lafiya zuwa kan iyakokinta.