An Sami Rubutaccen Sako Mai Shekaru 132 Cikin Wata Kwalba

A watan Janairu, an gano wata kwalba da ta kwashe shekaru 132, cikin wani ruwa dake kusa da wani tsibiri a kudancin Austarlia.

A cikin kwalbar, an sami wani rubutaccen sako da aka rubuta ranar 12 ga watan Janairun shekarar 1886, wanda wani matukin jirgin ruwa dan kasar Jamus, mai suna Paula, ya rubuta, mil 600 daga gabar tekun kasar Australia.

Wata mata mai suna Illman ce ta gano kwalbar yayin da yake tattaki a gabar tekun, ta kuma bayyanawa kafar yada labarai ta ABC, cewar “da na hangi kwalbar daga nesa ta bani shi’awa kwarai, shiyasa na yi tunanin matsawa kusa domin in ganta da kyau”.

A kwai wata takarda da aka murde aka daure ta da zare a cikin kwalbar, Illman da mijin ta sun kai kwalbar gidan adana kayan tarihi na kasar Australia inda masana da kwararru suka gano kasar da aka kera wannan kwalba.

Binciken ya nuna cewa an kera kwalbar ne akasar Netherland tun cikin karni na 19, tsakanin shekarar 1864 zuwa 1933, matukan jiragen ruwan kasar Jamus na jefa kwalabe da dama cikin teku inda wasu lokuta babban mai kula da jirgin kan rubuta suna da lambar jirgin a jiki.

Wannan abin al’ajibi ne matuka kamar yadda mai gidan Illman ya bayyana, kuma wannan wani bangare ne na bincike da kwararru ke gudanawar wa a yayin da suke gudanar da bincike akan albarkatun ruwa.

Mun sami wannan labara ne a shafin yanar gizo na yahoo.