Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Barawon Lambar Yabon karrama Manyan 'Yan Wasan Fina Finan Hollywood (Oscars)


Jami’an 'yan sanda a Los Angeles sun ce an kama mutumin da ake zargi da satar Lambar yabon gasar karrama masu sana’ar Fina Finan Hollywood da aka fi sani da Oscar na Frances McDormand bayan an kare bikin bada lambobin yabon a daren Lahadin da ta gabata.

An dai tsare wanda ake zargin ne mai suna Terry Bryant dan shekaru 47 da zargin babbar sata, a cewar mai magana da yawun 'yan sandan Rosario Herrera.

A wani faifan Video da kafar dillancin labarai ta AP ta dauka a yayin da ake gudanar da taron, ya nuna Bryant rike da lambar yabon ta Oscar in da yake alfahari 'yan kallo kuma sunai masa sowa.

Har yana cewa “To yara maza da mata” a yayinda yake tafiya da sauri ya kusa buge wata mata da ke gilmawa, Kana ya juwa hagunsa da damansa cikin sauri ya fice duk yana rike da lambar yabon ta Oscar.

'Yan sanda sun ce wani mai daukar hoto da ya dauki hotonBryant, bai iya gane Bryant daga cikin wadanda suka yi nasarar lambar yabon ba a yayin da ake gudanar da bikin saboda haka ya fara bin Bryant.

A yayin da aka tunkareshi Bryantt ya bada lambar yabon ba tare da wani kace nace ba, nan take jami’an tsaron da ke wurin suka tsare shi inda daga baya suka damka shi a hannun 'yan sanda daga baya dai an mayarwa McDormand lambar yabon ta.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG