Hukumomi a gabashin Congo sun ce akalla mutane talatin sun mutu kana wasu mutane dari biyu sun bata bayan wani jirgin ruwa ya nutse a wani tafki.
WASHINGTON, D.C. —
Kantomar yankin Inongo, Simon Mboo Wemba, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa da yammacin jiya Lahadi cewa galibin mutane da suka cikin jirgin ruwan da ya niste a tafkin Mai-Ndombe malamai ne.
Kantomar yace sun yi amfanin da jirgin ruwa ne zuwa karba albashin su ne saboda lalacewar hanyoyin yankin.
Sai dai nan da nan ba a iya gano adadin mutane dake cikin ruwan ba yayin da jirgin ya fada cikin yanayi mara kyau da yammacin ranar Asabar.
Amma jami’ai sun kiyasta akwai daruruwar mutane a cikin jirgin. Sama da mutane tamanin sun kubuta.