Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Gabashin Afrika Zasu Haramta Shiga Musu Da Kaya Masu Sauya Launin Fata


Man Shafawa
Man Shafawa

Kasashen Afrika ta Gabas suna shirin haramta shiga da sabulan wanka ko man shafawa ko kuma wani abu mai dauke da sanadarin hydroquinone, wanda ke sa mutum ya zama baturen karfi da yaji, sanadari dake tattare da matsalolin lafiya masu yawan gaske.

Majalisar dokokin kasashen Afrika ta Gabas a makon da ya gabata ta tabbatar da wani kuduri dake kira ga yankin baki daya kada a yi ko a shigo da kayan gyaran jiki mai dauke da sanadarin dake sauya launin fatai.

Kayan gyaran jiki mai sa fata tayi fari galibi ana yin sa ne da sanadarin hydroquinone, wanda ke kawowa fata matsaloli haka ma wasu sanadarai da aka harhada dake sauya launin fata suna iya zama ciwo.

Kasashen Ghana, Ivory Coast, Kenya, Nigeria, Rwanda da Afrika ta Kudu sun haramta ko kuma suna sa ido akan irin wadannan kaya, yayin da Tanzania ta haramta shiga da su kwata kwata a cikin kasarta.

Majalisar dokokin Afrika ta Gabas a makon da ya gabata ya tabbatar da kudurin haramta yi da kuma shiga da sanadarin hydroquinone a cikin yankin.

Suzan Nakawuki ‘yar majalisar dokokin yakin Afrika ta Gabas

Tace sanadarin mai sa fata tayi fari hydroquinone, ba mata kadai ke amfani da shi ba har da maza. Mun ga maza masu shafe shafe domin fatarsu tayi fari fiye da mata.Amma mun gano wannan abu ya zama babbar matsala, don haka dole a ja masa burki kafin ya ta’azzara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG