An harbe mutane 9 da wata karamar yarinya har lahira a kasar Kenya, yayin da tarzoma ta kara tsanani a wasu tungayen ‘yan adawa, bayan da a jiya jumma’a aka ayyana shugaba Uhuru Kenyatta a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasa.
Wani jami’in dakin ajiye gawarwaki na asibiti wand aba ya so a ambaci sunansa, yace an kai gawarwaki 9 dake dauke da raunuka na harbin bindiga zuwa dakin ajiye gawarwakinsu a Nairobi, babban birnin kasar, daga wata unguwa mai suna Mathare, inda madugun adawa Raila Odinga yake da karfi. Wani jami;in tsaron da shi ma ba ya son a ambaci sunansa ya fadawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa an kai gawarwakin.
Wani mazaunin unguwar ta Mathare, Wycliff Mokaya, ya fadawa kamfanin dillancin labaran AP cewa wani harsashi ya ratso kan barandar gidansa ya kashe diyarsa, mai shekaru 9 da haihuwa.
Yace yana kallonsu suna wasa da kawayenta, sai kawai ya ga ta fadi kasa.
Wani kwamandan ‘yan sanda na yanki, Leonard Katana, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na AP yau asabar cewa ‘yan sanda sun harbe suka kashe mutane biyu a lokacin wata tarzoma a bayangarin birnin Kisumu, inda Odinga yake da goyon baya mai karfi. Katana yace wasu mutane biyar kuma sun ji rauni a sanadin harbin bindiga a Kisumu.
An ji karar harbe harbe a Kibera, unguwar ‘yan share ka zauna mafi girma a Nairobi, da kuma wasu unguwannin marasa galihu na birnin.
Abubuwan da suka wakana a wadannan wuraren sun sha bambam baki daya da irin abubuwan da suka faru a yankunan da shugaba Kenyatta ke da goyon baya, inda magoya bayansa suka bazu kan tituna cikin annashuwa suna busa sarewa suna karkada tuta domin murnar sakamakon zaben.