An Sallami Shugaban Amurka Donald Trump Daga Asibiti

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Amurka Donald Trump yana shiga jirgi

Shugaban Amurka Donald Trump ya koma fadar White House jiya Litinin da yamma bayan shafe sa'oi 72 a kwance a asibitin sojoji na Walter Reed inda ya yi jinyar cutar COVID-19.

Shugaban na Amurka ya nuna ya sami lafiya tare da hawan matakalar benen fadar White House zuwa farfajiyar da ake kira Truman Balcony. Da isarsa, ya tsaya ya cire takunkuminsa ya sa aljihu daga nan ya daga babban yatsansa yana jinjinawa matukan jirgi mai saukar angulu na shugaban kasa Marine One yayinda yake shirin tashi daga harabar fadar White House. Daga nan shugaban kasar ya shiga fadar White ba tare da sake sa takunkumin ba, inda mutane suke jiran dawowarsa.