An Sako Wasu 'Yan Kamaru Hudu Daga Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya

Shugaban Kamaru-Paul Biya

Gwamnatin kasar Kamaru tace ‘yan tawaye a jamhuriyar Afrika ta tsakiya dake makwabta sun saki ‘yan kasar Kamaru guda hudu ranar Lahadi da suka yi garkuwa da su bara.

Mutanen hudu suna daga cikin ‘yan kasar Kamaru dari uku da ake zargin ‘yan tawayen da sacewa cikin shekaru biyu da suka shige, da kuma dubban shanu,

Al’ummomin kasar Kamaru dake kan iyaka suna kira ga gwamnatin kasar ta bada izini ga kungiyoyin sa kai su dauki makamai su kare kansu su kuma yaki ‘yan tawayen.

Binciken da kungiyar raya al’adu da ci gaban al’umma Mbororo ta gudanar wadda galibin membobinta makiyaya ne, na nuni da cewa, an sace ko kuma kashe a kalla shanu dubu takwas, aka kuma yi garkuwa da sama da mutane dari uku, yayinda kungiyar dake dauke da makamai ta janyo asarar kimanin dala miliyan hudu cikin shekaru biyu da suka gabata.