Har yanzu an kasa sanin adadin yara kanana bakin haure da ke cikin kasar Spain, ba tare da iyayensu ba – kuma hakan na dada zama matsala.
Tun watanni uku da su ka gabata, jami’an Spain su ka yi kiyasin cewa akwai yara kanana wadanda babu wani babba tare da su wajen 10,000 a cikin kasar – kuma kashe 70% daga kasar Morocco su ka fito. To amma an kuma gano cewa a shekarar 2018 kawai ma yara kanana bakin haure sama da 11,000 ne su ka kwararo cikin kasar, a cewar kungiyoyin jinkai.
“Aikin rajistar bakin haure yara wadanda babu wani baligi tare da su baya gudana da kyau,” a cewar wata kungiya mai zaman kanta mai suna Fundacion Raices, wadda ke kare hakkin bakin haure yara. Ta ce rashin sanin adadin yaran ba daidai ba ne ko kadan, kuma ya na da nasaba da rashin gaskiya a batun kare yara a kasar.
Jam’iyyar ‘yan ra’ayin rikau a Spain karkashin jagorancin Pablo Casado, na dada tsananta kyamar da ta ke nuna ma baki wajen kalamanta, al’amarin da ya sa Firaministan Spain Pedro Sanchez ya zarge ta da ruruta siyasa tsoratarwa.