An Sako Matar Ekweremadu Daga Gidan Yarin Birtaniya

Ike Ekweremadu, haagu da matarsa Beatrice, dama

An samu Beatrice da mijinta Sanata Ike Ekweremdu da laifin yunkurin safara da cinikin sassan jiki bil adama a London a watan Mayun 2023

An sako mai dakin tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Beatrice Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito.

A cewar rahotanni, sahihan majiyoyi sun tabbatar da komawar Beatrice Najeriya wacce kotun ta yankewa hukuncin shekaru shida.

An samu Beatrice da mijinta Sanata Ike Ekweremdu da laifin yunkurin safara da cinikin sassan jiki bil adama a London a watan Mayun 2023.

Kotun har ila yau ta samu likitin da aka hada kai da shi wajen yunkurin amfani da kodar wani matashi don sakawa ‘yar Ekweremadu da ke fama da larura koda.

An samu ma’auratan da laifin yaudarar matashin wanda suka dauko daga Legas zuwa London don ya ba da kodarsa.

Kotun ta Birtaniya ta yankewa Ekweremadu shekaru 10 ta kuma yankewa matarsa shekaru shida duk da cewa ta ce tana fama da larurar rashin lafiya.