Mukaddashin shugaban jami’ar, Dakta Aminu Ado, a madadin shugaban jami’ar, Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ya nuna godiya ga Allah (SWA) da sako daliban.
Dakta Ado ya kuma mika godiya ga uwargidan shugaban Najeriya, Remi Tunubu, a bisa kula da ta nuna kan lamarin.
A ranar Lahadi gwamnatin Najeriya ta mika daliban ga iyayensu bayan da suka gana da uwargidan shugaban kasa.
Daya daga cikin daliban mai suna Fatima Abdullahi ta bayyana cewa wannan abu kamar mafarki yake a gare su, kuma ba ta fatan ya sake faruwa a rayuwarsu.
Ita ma Rukayya Mohammed ta bayyana yadda aka sace su, inda ta ce suna cikin gida suna kwance sun kwanta tsakanin karfe biyu zuwa uku kawai sai suka ji mutane sun shigo cikin gidan kuma ba su san yadda aka yi suka shiga ba.
Ta kara da cewa, da farko sun zata barayin waya ne amma da suka yi kokarin guduwa suka fito waje sai suka ga ‘yan bindigar sun kewaye gidan, inda daga nan suka tisa keyarsu zuwa cikin daji.
Mohammed Saba, shi ne baban daya daga cikin dalibar da aka sace ya kuma tabbatar da sako daliban.
Ya ce tun ranar da suka kama yarsa, ‘yan bindgiar sun nemi kudin fansa na Naira miliyan biyar, inda aka rinka tattaunawa har aka dawo Naira miliyan biyu, amma dai daga bisa sun nemi Naira miliyan daya.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake sace dalibai a manyan makarantu ba, inda a wasu lokuta sukan shafe tsawon lokaci kafin a sako su.
Saurari cikakken rahoton Sani Shuaibu Malumfashi:
Your browser doesn’t support HTML5