Lauya na musamman Jack Smith ya sake shigar da wata sabuwar kara akan tsohon Shugaban Amurka Donald Trump dangane da zargin da ake yi cewa ya yi yunkurin sauya sakamakon zaben 2020.
Karar na dauke da tuhume-tuhumen farko sai dai a wannan karon an takaita zargin bayan da Kotun Koli ta ce tsoffin shugabannin suna da kariya.
Sabuwar tuhumar ta cire batun zargin tattaunawa da aka ce Trump ya yi da Ma’aikatar Shari’a.
A hukuncin da ta yanke wanda alkalai shida suka yi amanna da shi uku kuma suka nuna adawa, Kotun Kolin ta nuna cewa Trump na da wannan kariya a matsayinsa na tsohon shugaban kasa.
Wannan shari’a da ta sauya fasalin tuhume-tuhumenta, ta zamanto yunkuri na farko da masu shigar da kara suka yi na bin hukuncin da Kotun Kolin ta yanke dangane da batun kariya.