An Sake Kawo Wasu'Yan Najeriya 480 Daga Libya

A kalla matasa dari hudu da Tamanin ne suka koma Najeriya daga kasar Lybiya a ranar Lahadin da ta gabata.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewea za a tsugunar da dukkan su a wani sabon matsuguni da a bude a jihar Fatakwal, na wani dan lokaci kafin a mayar da su zuwa jihohinsu na asali.

Shugaban hukumar kai agajin gaggawa (NEMA) Engr. Mustapha Maihaja, da babban mai bada Matafiyan sun isa Najeriyar, da mai ba shugaban kasa shawara ta musammana akan harkokin da suka shafi cikin gida Mrs Abike, Dabiri-Erewa, da kuma mai wakiltar mai bada shawara kan harkokin tsaro na kasa ne suka yi rakiyar matafiyan.

Tawagar da ministan harkokin wajen kasar ya jagoranta ce ta yi yarjejeniyar mayar da bakin gida da gwamnatin kasar Libya.

Matafiyan sun isa filin saukar jirage ta jihar Fatakwal ne jiya lahadi da misalin karfe 5.05 na yamma.

Da yayi jawabi, shugaban hukumar kai daukin gaggawa NEMA ya bayyana cewa kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurni, an fara gudanar da ayyukan mayar da ‘yan kasar da suka makale a kasar Libya gida