Wasu manyan masu hannayen jari a kamfani Apple, sun nemi masu kera wayar hannu ta iPhone da su dauki matakan dakile tsanannin amfani da yara ke yi da hazikar waya ta ‘smart phone’ wanda hakan ke nuna illar amfani da kayyakin zamani na kafafen sada zumunta a tsakanin matasa.
A cewar kamfanin Jana Partners dake birnin New York, da kungiyar malamai ta jihar California, sun bukaci kamfanin Apple da su samar da wasu hanyoyin da matasan za su iya yin zabin wajen yakar yawan yin amfani da wayoyin.
Akwai matsayar da duniya ke tunanin dauka ciki har da dandalin samar da fasahohin zamani na Sillicon Valley, wajen samar da tsari mai nagarta da fito da hanyoyi da zasu inganta tsarin amfani da na’urorin zamani.
Wasikar na kunshe da wasu shawarwari da aka bukaci kamfanin na Apple, ya fitar da wasu tsare-tsare da zasu bayyana adadin shekaru da ire-iren abubuwa da kowane yaro ya kamata yayi amfani da shi a dai-dai yanayin shekarun sa.
Facebook Forum