Wata matashiya Aisha Shehu Kabara ta bayana irin gwagwarmayar da matsalolin da ta fuskanta a yayin da na fara jami’a kasancewar rashin kudin tafiyarda karatun ta.
Amma hakan bai karya mata gwiwa ba kasancewar neman ilimin ta sa a gaba
ta ce da ta shiga jami'a ba ta fara akan lokaci kamar kowanne dalibi ba sai da ta kusan cinye zangon farko kafin ta sami damar biyan har ta fara karatu ba, duk kuwa da cewa dukkanin takardunta ta samu nasara na shiga jami’a.
Wannan kuwa ya faru ne sakamakon rasa mahafinta da ta yi da wuri, wanda sai da mahafiyarta ta gudanar da kananan sanaoi kafin ta biya mata kudin makaranta har ta kammala kuma a yanzu ta kama sana’ar hannu gadan gadan.
Ta ce karatu ya zama wajibi, bayan kammala karatun ta na Diploma tunda aiki ya gagara ta shiga makarantar koyon dinkin ta ke kuma dinka zanuwan gado da kayayyakin kyale-kyale na mata.
Aisha ta ce ko ba komai tana fatan da sana’ar da take yi zata tara nan gaba ta sami digirinta ko idan ta sami aiki ta koma makaranta , tana mai shawarta ‘yan uwanta mata da su jajirce wajen neman ilimin zamani.
Facebook Forum