An sake kashe mutane takwas a kusa da birnin Jos

'Yan sanda a Jos sunce an kashe wani iyalin mutane takwas, a kusa da birnin Jos, jihar Plato a ranar asabar da dare.

'Yan sanda a tsakiyar Nigeria sunce an kashe iyalin mutum takwas a kusa da birnin Jos, inda ake fama da rikici ko kuma tarzomar kabilanci data addini akai akai.

A ranar asabar da dare aka kai wannan hari. Jiya lahadi jami'an yan sanda suka ce suna binciken wannan al'amari, amma kuma basu bada wani kari haske ba.

Wadanda aka kashe mata ne da mijinta da kuma 'ya'yansu guda shidda. Idan ba'a mance ba mutane da dama aka kashe, a mumunar arangamomin da aka yi tsakanin yan bangan Musulmi da Kirista da kuma rundunar soja a Jos a ranar Alhamis.

A ranar juma'a rundunar soja ta musamman da aka tura domin tabbatar da ana bin doka da oda a yankin, tace zata bari sojojinta sunyi amfani da karfi domin dakile tarzoma ko kuma kare kansu.

Mai magana da yawun rundunar soja yace, da sojoji suna inda aka yi kisan baya bayan nan, amma aka janye su domin mutane yanki sunyi zargin cewa sojoji suna karkashe mutane babu gaira babu dalili.

Mai magana da yawun rundunar soja Charles Ekeocha yace makamai sun dabaibaiye jihar. Yace matasa Musulmi da Kirista, ba wuya sun fara baiwa hamata iska, koda akan abinda bai taka kara ya karya ba.

Cikin shekaru goma da suka shige dubban mutane aka kashe a jihar Plato a saboda irin wadannan tarzoma.