Hukumomin Najeriya sun ce ambaliyar ruwan da ke faruwa nan da nan cikin gaggawa ta halaka mutane fiye da dari da biyu a yankin kudu maso yammacin kasar a makon da ya gabata.
Kungiyar Red Cross ta agajin jin kai da taimakon gajiyayyu ta Najeriya ta ce an kwashe daruruwan mazauna yankin bayan da wata ambaliya daga madatsar ruwan da ta rushe ta yi gaba da gidaje a garin Ibadan, mai kimanin tazarar kilomita dari da hamsin da birnin Ikko mai tashar jiragen ruwa. haka kuma ambaliyar ruwan ta rusa gadoji ukku a yankin.
Jami'ai sun ce rashin ingancin ginin gidaje da kuma rashin dacewar magudanun ruwa ko toshewar su, su ne su ka tsananta barazanar ambaliyar ruwan damuna a sassan Najeriya masu dimbin yawa.
Yanzu haka a Najeriya an shiga karshen damunar da galibi ke farawa daga watan mayu zuwa satumba. Hukumomin kasar Najeriya sun yi kashedi game da yawan ruwan saman bana na musamman.
Wata mummunar ambaliyar ruwan da aka yi a bara ta lalata gidajen mutane kimanin dubu dari biyar.