An Sake Jan Damarar Yaki Da Polio A Jihar Bauchi

An kaddamar da sabon zagayen aikin rigakafin cutar Polio na wannan watan a fadin jihar bauchi tare da tallafin hukumomin lafiya na duniya
An kaddamar da sabon zagayen yaki da cutar Polio na watan Satumba a fadin Jihar Bauchi, a ci gaba da yunkurin da ake yi na ganin an kawar da wannan cuta daga doron duniya.

Babban jami'in hukumar kiwon lafiya matakin farko a Jihar Bauchi, Dr. Nisser Ali Umar, ya roki jama'a da su bayar da hadin kai, yana mai tabbatar musu da cewa wannan maganin ba ya da illa, kuma ba ya da wani dandanon da zai sa yaro ya kyamace shi ko ya ji ba dadi idan an ba shi.

Ya roki masu gudanar da aikin rigakafin da su dauke shi tamkar na sadaukar da kai ba wai wanda suke yi don ana biyansu ko za a biya su ba.

Mai martaba Sarkin Dass, Alhaji Usman Bilyaminu Usman, shi ma ya roki iyaye da su bayar da cikakken hadin kai domin cimma nasarar gurin kawar da cutar Polio, yana mai fadin cewa an samu ci gaba sosai, kuma saura kadan ya rage a kawar da wannan cuta.

Amina Abdullahi Girbo, ta aiko mana da karin bayani daga Bauchi.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kara Jan Damarar Yaki Da Polio A Jihar Bauchi - 2:31