Shugaban Kwamitin Yaki da Cutar Polio ta Kasa a Najeriya, Dr. Abdul-Rahman Tunji Funso, ya fada lokacin da yake gabatar da rahoton ci gaban da aka samu wajen yaki da cutar cewa ya zuwa ranar 9 ga watan nan na Agusta, an samu sabbin rahotannin kamuwa da Polio guda 43 ne a jihohi 9, maimakon rahotanni 81 na kamuwa da wannan cuta da aka samu daga jihohi 11 a daidai wannan lokaci a shekarar da ta shige.
Sai dai kuma jami'in da kuma kungiyar nan ta Rotary mai bayar da tallafi wajen yakar cutar sun ce matsalar tsaron da ake fama da ita a arewacin Najeriya, ita ce ke kawo tafiyar hawainiya wajen kawar da wannan cuta.
Dr. Funso yace kashi 84 cikin 100 na dukkan sabbin kamuwa da cutar Polio da aka samu a bana sun fito ne daga jihohin Borno, Yobe, Bauchi da Kano, watau jihohin da suka fi fama da ayyukan 'yan kungiyar nan ta Boko Haram. Yaced babban kalubale ne ga kasar nan cewa har yanzu akwai yara kimanin dubu 200 da ba su samu maganin rigakafin Polio har sau uku da ake bukata don kaucewa kamuwa da cutar ba.