Gwamnati jihar Oyo ta rufe kasuwar kayan gwari da ke Sasa a garin Ibadan, kana ta kafa dokar hana fita a yankin da ke karamar hukumar Akinyele.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakaki gwamnatin jihar Oyo, Taiwo Adisa, da aka raba wa manema labarai, ya ce gwamanatin jihar Oyo ta kafa dokar hana fita daga shida na yamma zuwa karfe bakwai na safe a yankin.
Shugaban kasuwar Sasa, Alhaji Usman Idris, ya ce ko da yake gwamnati ta yi dai-dai na rufe kasuwar da sanya dokar hana fita a yankin na Sasa, amma matakin bai isa ba, idan ana son a magance rikicin.
Saboda lokacin da hankali ya tashi aka fara kone kone da ya janyo aka rasa rayuka, kafa doka daga karfe shida na yamma zuwa bakwai na safe ba zai magance rikicin ba.
Alhaji Usman ya kara da cewa dokar da suke sa ran zata yi maganim abin shi ne a ayyana doka sa’o’i ashirin da hudu, kuma abubuwan da suka faru marasa kyau, an yi asarar dukiyoyi, rayuka da shaguna da abubuwan da ba a rasa ba.
Amma rahotonni da muke samu yanzu suna cewa yawancin gidajen Hausawa da suke haya yaran unguwanni suna fasa gidajen sun debe kayayyakin su.
“Kuma ‘yan kungiyar tsaron Amotokun ne suka harbe mutane saboda lokacin da basu zo ba, ba a harbi kowa ba, ba a kone gida ko guda ba,” a cewar Alhaji Salisu.
Sai dai duk kokarin da muka yi na ji daga bakin kwamandan rundunar tsaro ta Amotokun, kanal Olayinka mai ritaya, hakar mu bata cimma ruwa ba, domin bai dauki kiran waya ba kan zargin kashe mutane da ake yiwa jami’ansa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, Gbenga Fadeyi, ya ce yanzu haka komai ya koma dai-dai kamar yadda aka saba, kana game da zargin wasoson kayayyakin jama'a ya ce a gayawa ‘yan sanda suna nan a kasa.
Saurari cikakken rahoton Hassan umaru Tambuwal:
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: jihar Oyo, Alhaji Usman Idris, Nigeria, da Najeriya.