Mutanen da suka sace Alhaji Salihu Wamako uban garin Wamako sun sameshi ne a gidan gonarsa dake da tazarar kilomita ashirin daga Sokoto fadar gwamnatin jihar.
Mutane hudu ne dauke da makamai suka kaiwa sarkin farmaki a gonarsa daga nan kuma suka yi awongaba dashi wani wurin da ba'a sani ba.
Rundunar 'yansandan jihar Sokoto ta tabbatar da aukuwar lamarin.Kakakin rundunar Al-Mustapha Sani shi ya bayyana aukuwar lamarin. Yace mutanen da mota suka je gidan gonarsa a Wamako wajejen karfe takwas. Inji jami'in 'yansandan sun baza mutanensu koina suna bincike domin a gano inda sarkin yake.
Shi Baraden Wamakon Alhaji Salihu Barade wa yake ga gwamnan Sokoto Alhaji Aliyu Magatakardan Wamako. Amma daya daga cikin 'yanuwan sarkin wanda kuma shi ne shugaban karamar hukumar Wamako Ahmed Abdullahi Kalanbaina yana ganin lamarin nada alaka da siyasa. Yace kila wata hanya ce aka bi game da kawo rudani saboda harakar zaben siyasa da za'a yi jibi.
Akan ko sace sarkin Bukuyum da aka yi wanda aka biya kudi kafin a sakoshi yana da alaka da abun da ya faru yanzu, Kalanbaina yace koda ma yana da alaka amma shi lamarin siyasa ya daukeshi. Da aka tambayeshi ko zasu biya fansa idan an bukaci su yi hakan sai Kalanbaina yace shi ba zai iya ce komi ba.
Wannan satar ta jefa mutane cikin rudani ganin yadda satar mutane da ba'a saba gani a arewa ba tana son ta zama ruwan dare gama gari.
Ga rahoton Murta Faruk Sanyinna.
Your browser doesn’t support HTML5