Kimanin makonni biyu da suka wuce ne, aka samu rubutaccen takardar barazana ga ‘yan makarantar Sakandare ta mata dake garin Malala, a karamar hukumar Dukku, akan cewa ‘yan Boko Haram zasu kai hari wannan makaranta.
WASHINGTON, DC —
Karamar hukumar Dukku dai, makwabiciyar jihar Yobe ce, kuma samun wannan barazana ke da wuya, aka kwashe yaran makarantar a cikin dare, aka mayar dasu gidajensu.
Bayan rufe wannan makaranta, gwamnati ta lura cewa baza ta iya sanin wa’adin da wannan lamari zai dauka, saboda haka yanzu an share kwanaki 10 da rufe makarantun gwamnati baki daya a jihar Gombe.
Gwamnatin jihar bata fito ta bayanna lokacin da za’a bude makarantun ba, sai dai ta saka daliban sunyi jarrabawarsu ta karshen wa’adin karatu, kafin a rufe makarantan.

Your browser doesn’t support HTML5