Jiya Laraba, sabon shugaban Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed, wanda aka fi sani da inkiyar "Farmajo" yayi rantsuwar kama aiki, a bikin ne shugaban yayi alkawarin daidaita al'amura a kasar da yaki ya daidaita, amma yayi gargadin cewa, aikin zai dauki shekaru masu yawa.
WASHINGTON, DC —
Shugaba Farmajo yayi kira ga 'yan kasar su taimaka masa wajen sake maido da doka da oda a kasar da yakin 'yar cikin gida tsakanin kabilu, da kuma mayakan sakai masu ikirarin musulunci, wadda fari ya kara ruruta matsalolin kasar.
Jim kadan bayan jawabin na shugaba Farmajo ne, Britaniya tayi alkawarin baiwa kasar gudumawa ta dala milyan 125, da zai hada da samar da abinci ga mutane da zasu kai milyan daya.
Shugabannin kasashe uku daga yankin ne suka halarci bikin kama aikin na sabon shugaban kasar, da kuma jami'an difilomasiyya masu yawa ne suka halarci bikin, ciki harda jakadan Amurka a Somalia Stephen Schawartz.