Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lamarin Karancin Abinci a Sudan Ta Kudu Na Kara Kamari


Sudan Ta Kudu.
Sudan Ta Kudu.

A martanin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) game da karancin abincin dake damun kasar Sudan ta Kudu, tace lamarin sai kara Kamari yake yi, hakan ya biyo bayan matsalar rashin zaman lafiya ne da kasar ke fama da shi tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen kasar.

Sai dai shugaba Salva Kirr, ya fada jiya talata cewa ma’aikatan jinkai zasu samu damar kaiwa ga daukacin fararen hula dake duk fadin kasar domin gudanar da ayyukan su.

Tun cikin shekarar 2013 ne dai kasar ta fada cikin rikici, wanda hakan yayi dalilin jefa mutanen da yawan su yakai dubu 100 cikin halin rashin abinci, musammam mutanen dake wasu sassan jihar Unity, Sai dai shugaba Kir yace gwamnatin sa zata tabbatar cewa maaikatan jinkai da kungiyoyin agaji basu samu cikas ba, wajen ganin sun kai ga mabukata a duk fadin kasar.

Yara da mata ne wannan iftila’in rashin abincin yafi shafa.

To sai dai duk da alwashin da shugaba Kirr ya sha na ganin maaikatan jinkai basu samu tangarda ba wajen gudanar da ayyukan su, duk da haka, babban jami’in dake kula da Ayyukan jinkai Mr Eugene Owusu, yace rashin tsaro na daya daga cikin abinda yake kawo wa maaikatan jinkai tarnaki na gaza kaiwa ga kauyuka domin baiwa mabukata taimakon da suke bukata.

Eugene yace, “zanyi anfani da wannan damar domin kira ga gwamnati dama ‘yan tawaye dama masu ruwa da tsaki wurin samar da zaman lafiya, dasu taimaka wa maaikatan jin kai domin samun damar kaiwa ga mutanen da ke bukatar taimako, domin ganin an ceto wasu bayin ALLAH.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG