Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Miliyan 20 a Kasashe Hudu Na Fuskantar Yunwa


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Gutierrez, jiya Laraba yayi gargadin cewa mutane milyan 20 a kasashe hudu suna fuskantar fuskantar 'yunwa idan ba hukumomin kasa da kasa sun dauki matakai na hana hakan aukuwa ba.

MDD ta ayyana Sudan ta kudu, da Somalia, da Yemel, da kuma sassan arewa maso gabashin Najeriya cewa suna daf da fadawa cikin matsanancin 'yunwa cikin watanni shid a masu zuwa. Hukumar ta duniya tuni ta ayyana mutane dubu dari daya a kananan hukunmomi biyu a jahar Unity a Sudan kudu suna fama da 'yunwa.

Babban magatakardan na MDD yace, ana bukatar kudi dala milyan dubu hudu da milyan dari hudu kafin nan da karshen watan gobe, watau mako hudu kacal daga yanzu. Domin ayyukan jinkai a shekarar baki daya, MDD tana bukatar dala milyan dubu biyar da milyan dari shida domin wadannan kasashe hudu.

Mr. Gutierrez yace a shirye MDD take ta fara aiki kan wannan matsala amma tana bukatar kudaden kamin ta fara aiki.

Cikin damuwa, Mr. Gutierrez yace zuwa yanzu MDD ta sami dala milyan 90 kacal cikin wannan adadi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG