Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sabbin shugabannin majalisun kananan hukumomin da aka zaba a karshen makon nan, wadanda a yau litinin ake sa ran su da kansilolinsu zasu fara aiki.
Hukumar zabe ta Jihar Kano, ta ce 'yan takarar jam'iyyar APC mai mulkin Jihar, ita ce ta lashe dukkan kujeru 44 na shugabannin kananan hukumomi, da kuma kujeru 484 na kansiloli a fadin jihar. Ma'ana babu daya daga cikin 'yan takarar sauran jam'iyyu 19 da suka shiga wannan zabe da ya samu nasara.
Masu rajin Dimokuradiyya dai na ci gaba da kushe yadda hukumar zabe ta jihar Kano ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a karshen mako, a daidai lokacin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da shugabannin kanananan hukumomi a jiya da maraice.
Wakilin Muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari, yace jinkirin samar da kayayyakin aiki, da rashin bayyanar jami’an zabe a tasoshi da cibiyoyin kada kuri'u, da kuma rashin fitowar Jama’a domin kada kuri’a kana da uwa uba dangwalen kuri’un a wasu cibiyoyin zaben ba tare da la’akari da ka’idojin zabe ba, na daga cikin abubuwa da suka zama ruwan dare a zaben shugabannin kananan hukumomi 44 da kansiloli 484 da hukumar zaben jihar Kano tayi a shekaran jiya asabar.
Wasu daga cikin mutanen da suka bayyana sun ce ba a gudanar da zaben ba, domin kuwa sun bayyana suka yini a rumfunan zabensu ba tare da ganin jami'an zabe ko kayan aiki ba.
Hukumar zaben ta jihar Kano karkashin jagorancin Farfesa Garba Ibrahim Sheka tace jam’iyyu fiye da 20 suka shiga zaben. Sai dai babbar Jam’iyyar hamayya a Najeriya ta PDP ta umarci ‘yayan ta da jama’ar gari dake goya mata baya su kauracewa zaben.
To amma a wani taron manema labarai da marecen lahadin nan, shugaban hukumar zaben ta jihar Kano Farfesa yace sun yi aikinsu tsakani da Allah kamar yadda suka yi rantsuwar zasu yi.
Sai dai kungiyoyin rajin dimokaradiyya na ganin abin daya faru a shekaranjiya asabar da sunan zaben kananan hukumomi tamkar fashi ne da makami a fagen dimokaradiyya.
Comrade Kabiru Saidu Dakata, shine babban daraktan kungiyar CAJA mai rajin tabbbatar da adalci da shugabanci na gari.
Yace abinda ya faru a Kano, misali ne dake nuna cewa hukumomin zabe na jihohi ba zasu iya gudanar da zabubbukan kananan hukumomi kamar yadda aka dora musu alhaki ba, ya kamata a rushe su a dora alhakin wannan zaben a kan hukumar zabe ta kasa, INEC.
Yace yayi farin ciki da shugaban hukumar zaben ta Kano ya fito ya fadawa duniya cewa sun kashe Naira miliyan dubu daya wajen gudanar da wannan zaben, tare da yin kira ga Hukumar EFCC da ta shigo cikin maganar domin ta gano ko ta yaya ne aka ce an kashe har naira miliyan dubu daya a wannan zaben da ba kamar zabe ba a Kano.
Your browser doesn’t support HTML5