A yau Litinin aka rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya, bayan da aka gudanar da zaben cike gurbi da kuma fuskantar matsin lamba kan ya gaggauta inganta yanayin tattalin arziki da tsaro.
washington dc —
Lamarin da wasu da dama ke korafin ya kara tabarbarewa a zamanin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari.
An rantsar da Tinubu ne a wani biki da aka yi a dandalin Eagle Square da ke babban birnin tarayya Abuja, wanda ya samu halartar manyan baki na ciki da wajen kasar.
Your browser doesn’t support HTML5
Biyu daga cikin manyan abokan hamayyar Tinubu a zaben watan Fabrairu na kalubalantar nasarar da ya samu a kan zargin magudi. A ranar Talata ne za a fara zaman kotun domin sauraren manyan hukunce-hukuncensu, inda ba a sa ran yanke hukuncin ba kafin watan Satumba.