Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Zaku In Mika Mulki – Buhari


Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya na matsuwa yayin da ranar mika Mulki ta 29 ga watan Mayu ke kara karatowa . A cikin wani jawabi da shugaban ya yi a baya bayan nan, ya nuna yadda ayyuka da halartar tarurruka da su ka yi masa yawa.

Yayin da al’ummar kasar ke dakon rantsar da zababben shugaban kasar Najeriya na 16 bisa tafarkin dimokuradiyya, Buhari, wanda zai mika ragamar mulki ga wanda zai gaje shi, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa yana sane da dimbin nauyin da ke gabansa.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da Hafsoshin Sojoji da kuma liyafa wanda aka gudanar a unguwar Asokoro dake Abuja. Shugaban wanda ya isa wurin cin abincin kusan sa'a guda a bayan da aka shirya, ya bayar da hakuri ga bakin da aka gayyata. Ya bayyana cewa yana fuskantar matsin lamba don gudanar da dimbin ayyuka da babban taron da ake shirye-shiryen gudanarwa a ranar 29 ga watan Mayu, baya ga sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

Taron bankwana
Taron bankwana

Ya ce: “Don Allah, zan so in ɗan rage kaɗan daga jawabin da aka shirya. Ina baku hakuri don na tsayar da ku a kalla rabin sa'a.

A tsawon mulkinsa, shugaba Buhari ya fuskanci kalubale da dama tun daga matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki. Duk da wadannan matsaloli, ya jajirce wajen yi wa al’ummar Nijeriya hidima gwargwadon iyawarsa. Yayin da ake shirin mika mulki, shugaban ya jaddada aniyarsa ta cika aikinsa da kuma tabbatar da mika mulki ga gwamnati mai zuwa cikin sauki.

A yayin taron, shugaba Buhari ya bayyana godiyarsa ga sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da na leken asiri bisa sadaukarwa da suke yi wajen tabbatar da tsaron kasa. Ya kuma tabbatar da kokarinsu na magance matsalolin tsaro da kuma gagarumar gudunmawar da suka bayar wajen gudanar da zaben kasar cikin nasara.

Taron bankwana
Taron bankwana

Sai dai shugaban ya jaddada cewa akwai bukatar a kara kaimi domin shawo kan matsalar rashin tsaro a kasar. Ya bukaci rundunar sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro da su jajirce wajen tunkarar kalubalen tsaro. Shugaba Buhari ya ba su tabbacin cewa, gwamnatinsa, duk da cewa ta kusa kawo karshe, za ta ci gaba da ba su goyon bayan da ya dace domin samun damar gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su yadda ya kamata.

Shugaban ya dauki lokaci mai tsawo wajen karrama jaruman da suka mutu, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan su, ya kuma amince cewa sadaukarwar da suka yi ba za ta taba zama a banza ba. Ya yabawa Hafsan Hafsoshin Tsaro, Ministan Tsaro, Hafsoshin Sojoji, da shugabannin sauran hukumomin tsaro bisa sadaukarwar da suke yi wa kasa.

Liyafar ta samu halartar manyan baki da dama da suka hada da Janar Lucky Irabor, babban hafsan hafsoshin tsaro, da kuma sakataren gwamnatin tarayya, da ministan tsaro, da wasu fitattun mutane daga sassa daban-daban. Tsofaffin hafsoshin soja da manyan jami'ai sun halarci taron, tare da wakilai daga cibiyoyin soji.

Yayin da ya rage ‘yan kwanaki, yanzu hankali ya koma kan tabbatar da mika mulki ba tare da wata matsala ba da kuma tabbatar da muradun al’ummar Najeriya.

XS
SM
MD
LG