Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Jawabin Ban-kwana Ga ‘Yan Najeriya


Taron bankwana
Taron bankwana

Muhammadu Buhari, yayin da yake gabatar da jawabinsa na karshe ga al'ummar kasar, a daidai lokacin da ya kawo karshen wa'adinsa bisa tafarkin dimokuradiyya.

A jawabin da ya yi, shugaban ya jaddada ci gaban dimokuradiyyar Najeriya da kuma nasarorin da aka samu a lokacin da ya ke kan mulki. Buhari ya nuna godiya ga al'ummar Najeriya tare da bayyana bukatar hadin kai da kuma ci gaban dimokuradiyya a kasar.

Shugaba Buhari ya yaba da yadda za a mika mulki cikin kwanciyar hankali, wanda ya bayyana a matsayin shaida na kara karfi da kuma cigaban dimokradiyyar Najeriya. Ya bukaci dukkan bangarorin da ke da ruwa da tsaki a zaben shugaban kasa da aka gudanar kwanan nan da su amince da hukuncin da kotu ta yanke tare da hada kai don gina Najeriya mai inganci.

Jawabin bankwana
Jawabin bankwana

Shugaban ya ci gaba da jawabinsa, inda yake yabawa da zabukan da aka gudanar, da jajircewa da dukkan ‘yan takarar shugaban kasa da jam’iyyunsu suka yi, inda ya jaddada burinsu na ganin Najeriya ta zama kasa ta gari.

Ya taya zababben shugaban kasa, abokinsa kuma tsohon amininsa na siyasa, Bola Ahmed Tinubu murnar nasarar da ya samu, inda ya bayyana kwarin gwiwarsa kan iya shugabancinsa na ganin ya kai Najeriya ga wani matsayi mai girma.

Jawabin bankwana
Jawabin bankwana

A yayin da ya ke yin tsokaci kan shekaru takwas da ya yi a kan karagar mulki, shugaba Buhari ya bayyana kudirinsa na inganta rayuwar talakawan Najeriya da samar da kasa mai hadin kai, da zaman lafiya da tsaro.

Ya ambaci sauye-sauyen da aka aiwatar don karfafa tsarin zabe, da tabbatar da gaskiya da kuma rage tasirin kudi a harkokin siyasa.

Buhari ya kuma yi tsokaci kan dorewar tattalin arzikin Najeriya, wanda ya kasance mai karfi ko da a cikin tabarbarewar tattalin arzikin duniya, ciki har da annobar COVID-19.

Ya kuma jaddada kokarin gwamnati na tallafa wa al’ummomin karkara, da karfafa mata, da samar da damammaki ga matasa. Shugaban ya yaba da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu wajen ciyar da tattalin arzikin kasar gaba, wanda ya kai ga kammala muhimman ayyukan more rayuwa.

Shugaban mai barin gado ya amince da ci gaban da aka samu wajen magance matsalar rashin tsaro, tare da rage yawan ayyukan ta'addanci, fashi da makami, da sauran ayyukan muggan laifuka a lokacin mulkinsa.

Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu lura da kuma mara wa jami’an tsaro baya wajen ganin an samar da yanayi mai kyau da tsaro.

Shugaban ya bayyana kudirinsa na ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa, wanda ya ke kallo a matsayin wani gagarumin cikas ga ci gaban Najeriya. Ya kuma bayyana yadda aka kwato kadarorin da aka samu ba bisa ka’ida ba da kuma dawo da kudaden da aka sace na kasar.

Shugaban ya kuma yaba da sauye-sauyen da ake yi na ma’aikatan gwamnati da nufin inganta ayyuka da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Bangaren kasa da kasa, shugaba Buhari ya lura da yadda Najeriya ke kara samun tasiri, inda ‘yan Najeriya ke rike da manyan mukamai na shugabanci a kungiyoyin duniya. Ya amince da rawar da majalisar dokokin kasar ke takawa wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya, ya kuma nuna jin dadinsa kan kwazo da kishin kasa.

A jawabinsa na rufewa, shugaba Buhari ya nuna jin dadinsa ga al’ummar Najeriya bisa goyon baya da addu’o’in da suka ba shi a tsawon mulkinsa.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar kasar cewa Najeriya na kan turbar daukaka, ya kuma bayyana kwarin gwuiwa kan yadda gwamnati mai jiran gado za ta iya dorawa kan ci gaban da aka samu.

Yayin da shugaba Buhari zai koma ya jiharsa ta Daura bayan kammala wa’adin mulkinsa, shugaban ya nuna gamsuwarsa, yana mai imanin cewa ya bar Najeriya cikin yanayi mai kyau fiye da lokacin da ya hau mulki a shekarar 2015.

Yanzu dai al’ummar kasar na dakon kaddamar da sabuwar gwamnati da kuma ci gaba. na tafiyar Nijeriya zuwa ga kyakkyawar makoma.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG