An Mika 'Yan Matan Cibok Ga Ministar Mata

Yayin da likiciyar da ta kula da lafiyar ‘yan matan makarantar sakandiren cibok da aka amso daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram, ga minister kula da harkokin mata Sanata A’isha Alhasan, ta shaidawa wakiliyar muryar Amurka Medina dauda bayanin cewa zata rike ‘yan matan har zuwa wani lokaci.

Da take bayani ministar mata ta bayyana cewa zata rike ‘yan matan har zuwa lokacin da aka bude makarantun gwamnati domin tura su makaranta inda zasu cigaba da neman ilimi.

An gudanar da wannan biki ne a gaban Dr Nicolas, wanda ya wakilci mukaddashin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya bada sakon cewa “a matsayinmu na gwamnati, zamu duk abinda zamu iya domin tabbatar da kun sani biyan bukatunku na samu ilimi, sana’oi da kuma sakewa a wuraren da kuka zaba koda tare da iyayenku ne, hakkin ku ne ba alfarma zamu yi maku ba”.

Kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen waje irinsu UNICEF,da hukumar kula da iyali ta majalisar dinkin duniya UNFPA, ne suka shirya wani katafaren gini da aka shiryawa ‘yan matan wurin zama, wato ‘yan mata biyu a kowane daki guda.

An kuma tanada masu dakunan karatu, da asibiti da dakunan cin abinci tare kuma da wuraren walwala kamar yadda Hajiya Kore Habib, jami’a a hukumar UNFPA, ta yi karin bayanin cewa kungiyar ta dauki dawainiyar aiwatar da ayyuka da dama domin kula da ‘yan matan

A halin da ake ciki yanzu, ‘yan matan na ci gaba da samun kulawar kwararru wadanda zasu dora su a kan hanyar da ta dace domin sauya masu tunani daga tashin hankalin da suka gani yauyin da suke a hannun ‘yan ta’adda.

Ga Medina Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Mika 'Yan Matan Cibok Ga Ministar Mata