Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Ta Bada Umurnin Kama Tsohon Gwamnan Jihar


Majalisar dokokin jihar Kebbi tana zargin tsohon gwamnan jihar Sa’idu Dakin Gari, da almubazaranci da aikata ba daidai ba a kwangilar ginin filin sauka da tashin jiragen sama na Ahmadu Bello dake jihar lamarin da yasa suka gayyace shi domin bada bahasi.

A wani zama da majalisar ta yi, ta umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar ya hanunta mata tsohon gwamnan ko ta halin kaka a sakamakon rashin halartar gayyatar da ta yi masa, kamar yadda mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Mohammad Buhari Alero, ya bayyana.

Aikin fadada filin jirgin zuwa wani matsayi ba sabon abu bane dominanj gina sababbi a jihar Jigawa, da Bauchi da kuma Gombe duk basu wuce Naira Biliyan goma sha daya zuwa goma sha biyu ba, amma abin mamaki ta jihar Kebbi da aka fadada kawai an kashe kudi sama da Naira Biliyan ashirin da wani a bu a cewar mataimakin kakakin, dan haka bincike ya nuna cewa akwai abubuwan da aka yi ba daidai ba.

Da yake amsa tambayar da wakilin sahsen Hausa na muryar Amurka, Murtala Faruk Sanyinna ya yi masa kan yadda jama’a zasu iya kallon lamarin tamkar bita da kulli ne ake yi masa kasancewar yawancin ‘yan majalisar sun fito daga jam’iyyar adawa, Muhammad Alero, ya bayyana cewar ba haka lamarin yake ba.

Tsohon gwamnan ya ce bai sami wata gayyata daga majalisar dokokin ba, kamar yadda tsohon mai bashi shawara kan sha’anin yada labarai kuma sakataren jam’iyyar PDP a jihar Malam Ibrahim Musa Argungu.

Ga Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG