Kasashen duniya sun zabura, suna sakawa gwamantin Syria da kawayenta sabuwar matsin lambar su ja burki ga bama-bamman da suke sakarwa garin Aleppo, don ma’aikatan bada agaji su sami sukunin shiga cikin birnin don tallafawa mazaunan garin da tarzomar ta rutsa da su.
WASHINGTON, DC —
A wajen taron da aka kira jiya a zauren MDD, a bisa shawarar kasar Canada, wanda kuma kasashe kamar 70 suka baiwa goyon baya ne, aka kudurta yin anfani da wata dabarar da ba safai akanyi anfani da ita ba wajen kiran taron gaggawa don a san yadda za’a bullowa du kata matsala da kan tuzgo.
Jakadan kasar ta Canada a MDD din, Stephane Dion yace dole a sami hanyar tabattarwa duniya cewa da gaske ake neman hanyar shawo kan wannan tarzomar.
Kwamitin tsaro na MDD ya fi share shekaru biyar yana neman hanyar da zai bi ya warware wannan rikicin na kasar Syria, ammakullum sai a fuskanci cikas.
Ko a kwanan nan, Rasha tayi anfani da karfin kuri’arta a karo na biyar dangane da wannan al’amarin na kasar ta Sham, inda ta hana a aiwatarda kudurin da kasashen turai suka gabatar kan tsaida wannan yakin da ake a cikin Aleppo.