WASHINGTON, DC —
A yanzu haka dai Gwamnatin jihar Neja, ta kwato motocin alfarma guda shida da tsohon Gwamnan jihar Dr, Mua’zu Babangida Aliyu, yayi awon gaba dasu.
Haka zalika bayanan sun nuna cewa harta tsohon mataimakin Gwamnan jihar an kwato wasu motoci daga hannun sa.
Sakataren yadda labarai na Gwamnan jihar Dr. Ibrahim Doba , “yace tabas motocin da aka kwato mallakar Gwamnatin jihar Neja ne kuma kwato hakkin jama’ar jihar Neja, hakkin ne da ya rataya akan mu.”
Kakakin tsohon Gwamna Babangida Aliyu, Mr. Israel Ebije, ya tabbatar da afkuwar hakar, wannan wata alama ce dake nuna cewa sabuwar Gwamnatin APC, a jihar Neja, ta shirya binciken tsohowar Gwamnatin da ta gabata.