An Kubutar Da Tsohon Sakatare Janar Na NFF Sani Toro

Ginin hukumar kwallon kafar Najeriya, NFF (Hoto: Facebook/NFF)

Tsohon shugaban hukumar ta NFF, Alhaji Aminu Maigari, wanda shi ma ya jagoranci hukumar a baya-bayan nan, ya tabbatar da sako Toro.

Rahotanni daga Najeriya na cewa an sako tsohon Sakatare Janar na hukumar kwallon kafar Najeriya NFF, Alhaji Sani Ahmed Toro da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a karshen makon da ya gabata.

A ranar Talata aka sako Toro.

Toro da wasu abokanan tafiyarsa biyu sun fada hannun masu garkuwa da mutane yayin da suke hanyarsu ta komawa Bauchi daga Abuja, babban birnin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a yankin karamar hukumar Akwanga da ke jihar Nasarawa.

Tsohon shugaban hukumar ta NFF, Alhaji Aminu Maigari, wanda shi ma ya jagoranci hukumar a baya-bayan nan, na daga cikin wadanda suka yi jagora wajen ganin an kubutar da su kamar yadda ya tabbatar ma Muryar Amurka.

Yayin wata hira da Maigari ya yi da Muryar Amurka, ya fada cewa ba a biya ko sisi ba aka sako Toro da mutanen.

“Ba a ba da ko kwabo ba, addu’a kawai muka yi ta yi.” In ji Maigari a lokacin da aka tambaye shi ko an biya kudi n fansa.

Abdulkadir Sani Toro, da ga Toro, ya kara tabbatarwa da Muryar Amurka cewa an sako mahaifin nasu.

Ya kara da cewa mahaifin nasu yana cikin koshin lafiya.

A halin da ake ciki kuma, an samu rahoton da ke nuni da cewa an sako Sarkin Kauyen Zira ,Yahaya Saleh da dansa mai suna Habibu Saleh Abubakar, su ma dai a yau din ne aka sako su.

Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad daga Bauchi:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kubutar Da Tsohon Sakataren Janar Na NFF Sani Toro - 2'49"