Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai farmaki tare da kona ofishin shelkwatar jam’iyyar APC na jihar Kano.
An kona ofishin wanda ke kan titin Maiduguri a cikin birnin Kano, na bangaren tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau da safiyar yau Alhamis, kuma ana zargin ‘yan dabar sun fito ne daga bangaren jam’iyyar ta APC da ke adawa da bangaren na Shekarau.
Wannan lamari dai na zuwa ne kwana 2 bayan da wata babbar kotu a Abuja ta tabbatar da shugabannin jam’iyyar ta APC da aka zaba daga bangaren na Sha’aban Sharada da Malam Shekarau, a zaman halatattun zababbin shugabanni, inda kuma ta rusa zaben da bangaren gwamna Abullahi Umar Ganduje suka gudanar.
A cikin hukuncin na kotun, mai shari’a Hamzat Muazu ya ba da umarnin hannunta musu dukkan lamurran shugabancin jam’iyyar.
Idan za’a iya tunawa a ranar 31 ga watan Yulin wannan shekara ne bangaren jam’iyyar APC na gwamna Ganduje ya ba da sanarwar dukkan ‘yan takarar shugabancin jam’iyyar da suke daga bangarensu, da cewa su ne halatattun shugabanni da aka zaba ta hanyar sasantawa.
To sai dai kuma Sharada ya garzaya kotu, inda ya kalubalanci wannan sanarwa, bayan da su ma sun gudanar da zabe a na su bangare.