Jami’an tsaron sunce an fara kai hare-haren ne a daren jiya litinin, lokacinda wata motar ‘yan sandan ta taka wata nakiya da aka binne a kasa a kusa da kauyen Yumbis, inda ‘yan sanda akalla 3 suka jikkata. Jami’an kuma sunce abokan aikinsu dake kan hanyar kai gaji ga dan sandan da ya jikkta suma ‘yan yakin sa kai suka yi musu kwantar bauna, abinda ya janyo mummnan musayar wuta.
Shugaban ‘yan sandan garin Garissa dake Kenya, Abdrashid Abdullahi, ya gaya wa muryar Amirka cewa an kashe dan sanda daya wasu guda biyu kuma sun jikkata. A lokacin da aka yi musayar wutar.
Garin na Garissa na kusa da wurin da ‘yan al-Shabab suka kai hari a wata kwaleji cikin watan da ya gabata inda suka kashe dalibai 148.
‘Yan kungiyar al-Shabab sunce ‘yan sanda 20 aka kashe a hare-haren da aka yi jiya litinin, amma ‘yan sanda da jami’ai sun musanta rahoton.