An Kashe Tsohon MInistan Kudi kuma tsohon Jakadan Lebanon a Amurka, Mohammed Chata

Farar hula da jami'an tsaro suka hallara a dai dai inda aka kai harin bam da ya halaka tsohon ministan kudinda wasu jami'ai biyar.

An kashe tsohon ministan kudi na Lebanon Mohammed chatah, mutuminda yake matukar sukar lamiri kan shugaban kasar Syria Bashar al-Assad, a wani gagarumin harin bam da aka yi amfani da mota aka kai masa a tsakiyar Beiruit.
An kashe tsohon ministan kudi na Lebanon Mohammed chatah, mutuminda yake matukar sukar lamiri kan shugaban kasar Syria Bashar al-Assad, a wani gagarumin harin bam da aka kai da mota a tsakiyar Beiruit.

Wasu mutane biyar suma sun rasa rayukansu, kimanin wasu 70 kuma sun sami raunuka a fashewar da ta auku jiya juma’a, wanda ya auku bayan jerin wasu hare hare da aka yi shekara daya ana aunawa kan shi’a da kuma sunni a Lebanon.

Chatah wanda dan sunni ne tsohon babban mai bada shawara ne ga tsohon PM kasar Sa’ad Hariri. Ya kuma taba zama jakadan kasar a Amurka.

Wakiliyar MA Margret Basheer wacee take Beiruit tace masu kallon al’amuran yau da kullum ba sa zaton chatah dan shekaru 62 da haifuwa zai kasance wand a za a so yiwa kisan gilla.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yayi Allah wadai da harin bam din, ya kira kisan Chatah da cewa “mummunan laifi kuma ragaye ne suka kai hari kan adilin mutum. Kerry yace mutuwar Chatah babbar hasara ce ga mutan Lebanon kuma tilas ne a hukunata wadanda suka kai harin.

Sa’a daya kamin mutuwarsa, Cahatah ta tura sako ta dandalin Twitter yana sukar Syria da kungiyar mayakan sakai ta Hezbollah,wacce ta tura mayaka wadanda suke goyon bayan shugaba Bashar al-Assad a fagen yakin basasar kasar da ake fafatawa.

Zuwa yanzu dai babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai wannan hari.