Mai shigar da kara na kasar ya sanar da cewa, wani dan adawa a kasar Chadi na cikin mutane da dama da aka kashe yayin da yake jagorantar harin da aka kai kan hukumar tsaron kasar a babban birnin kasar cikin wannan mako.
Harin dai ya nuna tabarbarewar halin da ake ciki a kasar Chadi da ke tsakiyar Afirka gabanin zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 6 ga watan Mayu.
Shugaban da aka kashe, Yaya Dillo, dan’ uwan shugaban kasar ne na yanzu kuma dan takara mai karfi a zabe mai zuwa. Shi ne ya shugabanci jam'iyyar Socialist Without Borders, wacce ta kai harin a ranar Laraba a Hukumar Tsaro ta Kasa.
Mai shigar da kara na jihar, Oumar Mahamat Kedelaye ya ce Dillo na daga cikin wadanda aka kashe amma bai yi karin haske kan yadda aka kashe shi ba ko kuma ya bayyana wanda ya harbe shi.
Maharan dauke da muggan makamai cikin motoci sama da 10, sun taso ne su ka kutsa ofisoshin hukumar da ke N’Djamena babban birnin kasar. Akalla mutane goma sha biyu ne aka kama kuma ana kan gudanar da bincike, in ji Kedelaye.
Harin ya biyo bayan kama sakataren kudi na jam'iyyar adawa a ranar Laraba da ta gabata bisa zargin yunkurin kashe shugaban kotun kolin kasar.
Shugaban rikon kwarya na kasar Chadi, Mahamat Deby Itno dai ya kwace mulki ne bayan da aka kashe mahaifinsa da ya kwashe sama da shekaru 30 yana mulkin kasar a yakin da ake yi da ‘yan tawaye a shekara ta 2021. A shekarar da ta gabata kuma gwamnatin kasar ta sanar da tsawaita wa’adin mika mulki na watanni 18 na tsawon wasu shekaru biyu, wanda ya yi sanadiyar zanga-zanga a fadin kasar.
~ AP