Rikicin ya barke ne kwana guda bayan da hukumar zaben kasar Chadi ta sanya ranar 6 ga watan Mayu, a matsayin ranar gudanar da zaben shugaban kasa, wanda shi ne na farko tun bayan da shugaban rikon kwarya Mahamat Idriss Deby Itno ya karbi mulki a shekarar 2021.
Ba a bayyana ko tashin hankalin yana da nasaba da sanarwar zaben ba. Sanarwar da gwamnati ta fitar ta ce harin da aka kai kan hukumar tsaron kasar “yunkuri ne na kashe shugaban kotun koli.” Ta ce an kama mutane da dama da ake zargin an kuma ci gaba da neman wasu da suka tsere.
Sanarwar ta dora alhakin harin kan jam'iyyar Socialist Party Without Borders da kuma shugabanta Yaya Dillo.
Babban sakataren jam'iyyar ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa an samu asarar rai ne lokacin da sojoji suka bude wuta kan gungun 'yan jam'iyyar a kusa da hukumar tsaro.
Ya ce an harbe wani dan jam’iyyar Ahmed Torabi a ranar Talata kuma an kai gawarsa hedikwatar hukumar. A safiyar Laraba, a cewar babban sakataren, ‘yan jam’iyyar da ‘yan uwan Torabi sun je nemo gawarsa a hukumar inda sojoji suka yi musu luguden wuta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Wani dan jaridan Muryar Amurka Moki Edwin Kindzeka ya ce mutanen da suka tsorata da harbin bindiga a N’djamena na tserewa ta kan iyaka zuwa gabashin Kamaru ranar Laraba.
Ofishin jakadancin Amurka a kasar Chadi ya shawarci Amurkawa a N’djamena da su kaucewa unguwar Klemat, kusa da hedkwatar jam’iyyar.
Dandalin Mu Tattauna