Wasu 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba sun bindige shaihin malamin cikin dare tare da matarsa da dansa
WASHINGTON, DC —
Wasu 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba sun bindige suka kashe shaihin malamin Sunni, Sheikh Muhammad Awwal Albani Zaria, cikin dare a garin Zaria. An kashe shi tare da matarsa da dansa. <br /> <br /> Wani mukarrabin malamin, Sheikh Abbas Isa Lauya Zaria, ya tabbatarwa VOA abkuwar wannan lamarin.