An Kashe Osama Bin Laden

Osama bin Laden

Osama bin Laden

Majiyoyi sun ce dakarun Amurka sun kashe shugaban kungiyar al-Qa'ida, Osama bin Laden, a wani gida a babban birnin Pakistan

Shugaba barack Obama na Amurka yana shirin gabatar da jawabi ga duniya domin bayyana cewar Ajmurka ta kashe mutumin da aka fi nema ruwa a jallo a duniya, Osama bin Laden, kuma gawarsa tana hannun Amurka a yanzu haka.

Wannan al'amari zai zo kusan shekaru 10 a bayan mummunan harin da 'yan al-Qa'ida suka kawo kan Amurka a ranar 11 ga watan Satumbar 2001.

Wasu majiyoyin kafofin labarai na Amurka su na fadin cewa an kashe Osama bin Laden cikin wani gida a bayangarin Islamabad, babban birnin Pakistan.