Shugaban 'yan sandan kasar Haiti ya ce an kashe mutane hudu da ake zargi da kisan shugaba Jovenel Moise jiya Laraba a wata musayar wuta da ‘yan sanda.
WASHINGTON DC —
Cif Leon Charles ya shedawa manema labarai a Port-au-Prince cewa na kame wasu mutum biyu da ake zargi, wadanda ya bayyana a matsayin sojojin haya a lokacin harbe-harben.
An kubutar da 'yan sanda uku da wadanda ake zargi da kisan gillar suka yi garkuwa da su. Charles bai ba da wani karin bayani game da aikin ba.
Jim kadan bayan kisan Moise an kaddamar da farautar wadanda suka aikata kisan a yayin wani samame kan gidansa a wata unguwar masu hannu da shuni a wajen Port-au-Prince.
Jakadan Haiti a Amurka, Bocchit Edmond, ya fada wa manema labarai a Washington cewa an rufe iyakar Haiti da Jamhuriyar Dominican da kuma filayen jiragen sama.